Mu ne Matasa ‘Yan Kudancin Kaduna Masu Dauke da Fitila (SKYTB) – Masu Haska Hanya. Masu Jagorantar Sauyi. A yau, muna ci gaba da daga murya cikin hadin kai da alfahari, domin nuna cikakken goyon bayanmu ga wani mutum mai hangen nesa, gaskiya, jaruntaka da aiki—Zakaria Dauke, wanda aka fi sani da kiransa Fari Doki Sabo da FARIN zuciyar sa.
A takarar kujerar Sanata na Kudancin Kaduna a shekarar 2027, Zakaria Dauke ba kawai ɗan takara bane—shi ne zabi na gaskiya. Mutum ne da rayuwarsa ke nuna ƙarfin hali cikin tawali’u, jagoranci mai cike da tausayi, da ci gaba mai ma’ana da hangen gaba.
Read More

